Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya ce takar shugaban kasa ba “wasan kwamfuta” ba ne, yayin da yake mayar da martani kan rokon da wasu kungiyoyin matasa suka yi masa na ya tsaya takara a zaben 2027.
Jonathan ya fadi hakan ne a ranar Alhamis yayin da wasu kungiyoyin matasa suka ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja domin karfafa shi ya sake tsayawa takarar shugaban kasa.
Da yake amsa rokon, tsohon shugaban kasar ya ce zai yi shawarwari sosai kafin ya yanke wani hukunci, yana mai jaddada cewa shugabanci yana bukatar yin tunani sosai.










































