ADC ta rage kudin fom din takara, ta fitar da sabon jadawalin zaben fidda gwani na 2026

ADC ADC 750x430

Jam’iyyar ADC ta rage kudin fom din takar Shugaban Kasa zuwa Naira miliyan 90 tare da fitar da sabon jadawalin zaben fidda gwani na shekarar 2026.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa jam’iyyar a baya ta kayyade kudin fom din takar Shugaban Kasa a Naira miliyan 100.

Sakataren Yada Labaran jam’iyyar na Kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Abuja, ya ce rage kudaden ya biyo bayan tattaunawa da shugabannin jam’iyya, masu neman takara da masu ruwa da tsaki daga fadin kasar.

A cewar NAN, a karkashin sabon tsarin, fom din takar Shugaban Kasa yanzu Naira miliyan 90 ne, na Gwamna Naira miliyan 30, sai na Sanata Naira miliyan 10 da Majalisar Wakilai Naira miliyan 5, yayin da na Majalisar Jiha Naira miliyan 2.

NAN ta kuma ruwaito cewa jam’iyyar ta ci gaba da tsarin rangwame, inda matasa masu shekaru 18 zuwa 35 ke samun rangwame na kashi 50, yayin da mata da masu nakasa ke samun kashi 25.

Bisa ga jadawalin, za a fara siyar da fom din takara daga 1 zuwa 4 ga Mayu, yayin da za a karbi fom din da aka cika daga 6 zuwa 13 ga Mayu.

“Tantance masu neman takara an shirya shi ne daga 14 zuwa 15 ga Mayu, sakamakon kuma za a fitar da shi a 17 ga Mayu, yayin da za a saurari korafe-korafe kara daga 18 zuwa 19 ga Mayu.

“Za a fitar da jerin sunayen masu neman takara da aka amince da su a 20 ga Mayu, gabanin zaben fidda gwani na Majalisar Jiha, Majalisar Wakilai da na Sanatoci a ranar 21 ga Mayu.

“Za a gudanar da zabben fidda gwani na Gwamna a 22 ga Mayu, yayin da na Shugaban Kasa za a yi shi a ranar 23 ga Mayu, sannan za a gudanar da tarukan NEC da na Babban Taron Jam’iyya.

“An shirya taron Kwamitin Zartarwa na Kasa a ranar 25 ga Mayu, yayin da za a gudanar da Babban Taron Musamman na Kasa a ranar 26 ga Mayu, 2026,” in ji Abdullahi.

Ya kara da cewa wadannan sauye-sauye na zuwa ne bayan tattaunawa mai domin karfafa dimokuradiyya a cikin jam’iyya, inganta shigar da kowa da kuma ba da dama ga masu neman takara.

Mai magana da yawun jam’iyyar ya bukaci dukkan masu neman takara da masu ruwa da tsaki da su bi sabon jadawalin da ka’idojin da aka fitar ba tare da bata lokaci ba gabanin babban zaben 2027. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here