Gwamnatin Kano ta duba wuraren renon tsiro, a shirin da take na shuka bishiyoyi miliyan 10 a 2026

WhatsApp Image 2026 04 28 at 07.57.06 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta kara kaimi wajen habaka dorewar muhalli ta hanyar fara gangamin shuka bishiyoyi, tare da shirin raba miliyoyin tsiro a fadin jihar.

A wata sanarwa da aka sanya wa hannu a ranar Litinin, Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi, Dr Dahir M. Hashim, ya ce ana aiwatar da shirin karkashin jagoranci da amincewar Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya dauki aniyar shuka bishiyoyi miliyan 10 a wannan shekara.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa kwamishinan ya bayyana cewa kwanan nan ya kai ziyarar duba wuraren renon tsiro a kananan hukumomin Gwarzo da Dawakin Kudu domin tantance ci gaba da tabbatar da shirye-shirye don aikin rabon da za a yi a babban mataki.

A cewarsa, a halin yanzu wuraren renon suna da tsiro iri-iri, ciki har da zogale, dorawa, lemon tsami, darbejiya, mangwaro, lemon zaki da goba, wadanda za a raba domin shuka wa a sassa daban-daban na Jihar Kano.

“Muna da iri-iri kamar zogale, dorawa, lemon tsami, darbejiya, mangwaro, lemon zaki da goba, wadanda muke niyyar rabawa don shuka a sassa daban-daban na jihar,” in ji shi.

Dr. Hashim ya yi kira ga kungiyoyin al’umma da makarantu da su yi amfani da damar shirin ta hanyar neman tsiro da zarar an fara aikin.

Ya kuma bayyana cewa kungiyoyin da ke da sha’awa za a bukaci su cike fom din da za a samar ko su rubuta kai tsaye zuwa ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi.

Kwamishinan ya kara da ce, shirin wani bangare ne na kokarin da gwamnatin jihar Kano ke yi don yaki da lalacewar muhalli da magance tasirin sauyin yanayi ta hanyar dasa itatuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here