PRP ta musanta ikirarin bangaranci a jam’iyyar

PRP logo gold

Jam’iyyar PRP ta yi watsi da ikirarin rabuwar kai a tsakanin ‘yan jam’iyyar, tana mai gargadi kan abin da ta bayyana a matsayin kokarin wasu daga waje na kutsawa tare da tayar da hargitsi a jam’iyyar a daidai lokacin da take cewa tana samun karfi a siyasance a fadin kasa.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa wani bangare na jam’iyyar ta PRP ya ki amincewa da sakamakon taron kasa da aka ruwaito an gudanar kwanakin baya a Abuja, inda suka bayyana shi a matsayin taron bogi kuma suka zargi wani bangare da kokarin karbe ikon jam’iyyar don muradun wasu manyan mutane gabanin zaben shekarar 2027.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Kano ranar Litinin, bangaren karkashin PRP-Vanguard Collective, ya soki fitowar wani sabon shugaban jam’iyya na kasa daga abin da ya kira “bangaren Falalu,” yana mai jaddada cewa lamarin ya saba wa kundun tsarin mulkin jam’iyyar da tushen akidarta. Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Abdulmajid Yakubu Daudu, ya soki Hakeem Baba-Ahmed musamman, wanda ya yi ikirarin cewa bai taba zama dan jam’iyyar PRP ba amma yanzu “yana ikirarin yana shugabantar al’amuranta.”

Da yake karin bayani a ranar Talata, Sakataren yada labarai na jam’iyya na kasa, Muhammed Ishaq, a cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja, ya ki amincewa da rahotannin da ke nuna samun wani bangare da ke aiki da sunan PRP-Vanguard Collective.

Ya ce, “Wadannan mutanen da ake kira ba su da wani tasiri kuma shugabancin PRP ko ‘yan jam’iyyar ba su san su ba. Me ya sa yanzu muke fara jin wannan ikirarin, a daidai lokacin da PRP ke samun karin kulawar siyasa kuma take kara samun karfi?

“A bayyane yake cewa wadannan kawo cikas kokari ne na wasu masu bukata na rage ci gabanmu, amma ba za mu yi sanyi ba.” Inji sanarwar.

“Muna so duniya ta sani cewa ba za mu nuna gazawa ba, kuma ba za mu girgiza ba saboda tsoratarwa, karkatar da labarai, ko farfaganda. Mun shirya don kare gaskiya babu ruwanmu da kirkira. Kada a yi kuskure hakurinmu bai kamata a dauke shi a matsayin rauni ba.”

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake kara harkokin siyasa da sake tsari gabanin zaben shekarar 2027, tare da jam’iyyu da dama da ke fama da rikice-rikicen cikin gida da tattaunawar hadaka.

A wannan yanayi, PRP ta ce ba za a ja ta cikin abin da ta kira kokarin da aka shirya don raunana tsarinta ko kawo cikas ga tasirinta da ke karuwa ba.

“Mugunta da rashin hakurin wadannan kungiyoyi na iya rufe musu ido ga gaskiya, amma niyyar mu ta tsaya tsayin daka,” in ji Ishaq.

An kafa jam’iyyar PRP a shekarar 1978, inda ake daukar ta a matsayin daya daga cikin tsofaffin jam’iyyun siyasa da suka tsira a Najeriya, mai tushe a cikin jam’iyyun siyasa masu ci gaba na Jamhuriya ta Biyu.

Jam’iyyar sau da yawa tana nuna kanta a matsayin dandali da aka gina a kan adalci na zamantakewa da manufofi masu goyon bayan jama’a, duk da cewa tana kokarin sake gina martabarta a kasa a yanayin siyasar yanzu.

Da take sake tabbatar da juriyarta na tarihi, jam’iyyar ta ce tsira daga mulkin soja da rikice-rikicen siyasa na shekaru da dama ya nuna karfinta.

“Mun shirya, kuma mun fara, gaba tana ga wadanda suka tsaya tsayin daka a kan gaskiya da ka’ida. PRP ta ci gaba da jajircewa ga akidunta, ‘ya’yanta, da al’ummar Najeriya, ba za a karkatar da mu ba, ba za a hana mu ba, kuma za mu ci gaba da tafiya gaba har sai an cimma fansar Najeriya ta gaskiya,” in ji sanarwar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here