Hadakar jam’iyyun adawa a Najeriya sun cimma matsaya a hukumance kan tsayar da dan takara daya don kalubalantar jam’iyya mai mulki ta APC a babban zaben shekarar 2027.
Matsayar, wanda aka yiwa lakabi da ‘Ibadan Declaration’, an cimma ta ne a wajen wani babban taro da jam’iyyun adawa suka yi a ranar Asabar 25 ga watan Afrilun shekarar 2026 a babban birnin Oyo.
Jam’iyyun adawan sun hada da PDP da ADC da PRP da NNPP da NDC da LP da Accord da APM da AA da DLA da YP da ADP da kuma ZLP.
Da yake karanta takardar bayan taron a madadin shugabannin taron, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Taminu Turaki (SAN), ya ce daukar wannan mataki ya zama wajibi ne domin tsaratar da Najeriya daga irin makurar da jam’iyyar APC ke yi mata.
Hadakar jam’iyyun adawar sun bayyana cewa babban abin da suka sag aba shi ne kubutar da Najeriya daga zama kasa mai jam’iyya daya. Duk da cewa APC ta nuna shugaban kasa Bola Tinubu ne dan takararta a zaben 2027, jam’iyyun hadakar sun shirya kalubalantar hakan.
“Ya kamata mu tsayar da dan takarar shugaban kasa daya a zaben 2027, wanda zamu amince kuma mu goy awa baya a matsayinmu na jam’iyyun adawa domin tsiratar da wannan kasa da kuma ‘yan kasar da suka kasance cikin tsananin wahala tsawon lokaci.” Inji takardar.
Taron ya kuma yi kakkausar suka ga shugabancin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), sun kuma kada kuri’ar rashin kwarin gwiwa ga shugabancin Farfesa Joash Amupitan, inda suka zarge shi da goyon bayan jam’iyya mai mulki.
Haka zalika, sun yi gargadin ci gaba da zaman shugaban a matsayin shugaban hukumar babbar matsala ce da ka iya kirkirar tashin hankali a kasa. Inda suka ce dole a maye gurbinsa da wanda bashi da bangare don tabbatar da adalci.
Taron ya bukacin abubuwa masu yawa, cikin kuma harda bukatar Majalisar Kasa kan ta yi gaggawar yin gyara kan dokar zabe ta shekarar 2026.
Haka kuma, hadakar jam’iyyun sun caccaki sharudan zabukan fidda gwani na jam’iyyu, inda suka bukaci da a tsawaita shi har zuwa karshen watan Yuli.
Jam’iyyun sun kuma bukaci da ayi gaggawar sakin duk ‘yan adawar da ake rike da su a halin yanzu.
Daga karshe, sun yabawa Gwamna Seyi Makinde saboda ya karbi bakuncin wannan muhimmin taro da aka yi a Jihar Oyo. Wakilai da yawa suna ganin wannan taron wani mataki na tarihi da zai taimaka wajen shirin zaɓen 2027.












































