Wata kotun tarayya da ke zama a Abuja ta soki karar neman kare hakkin dan Adam da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar a ranar Laraba.
An shigar da karar ne kan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Laifuka Masu Alaka da ita (ICPC) da wasu mutane hudu.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta nuna kura-kurai a cikin karar bayan lauyan El-Rufai, Ugochukwu Nnakwu, ya sanar da kotun cewa bai samu damar kai wa alkalin kotun majistare takardar kara ba, wanda aka sanya a matsayin wanda ake kara na biyu a cikin shari’ar.
Lokacin da aka kira karar a ranar Laraba, dukkan bangarorin shari’ar sun halarta a kotu, sai dai wanda ake kara na biyu (alkalin majistare).
Lauyan ICPC, Isaac Akwo, ya roki kotu da ta dage sauraron shari’ar zuwa karfe 12 na rana domin babbansa, Abdu Mohammed, SAN, wanda ke kotun koli, ya halarci shari’ar, amma mai shari’a ta ki amincewa saboda tana da wani taro.
Mai shari’a ta tambayi halin da ake ciki game da wanda ake kara na biyu, inda lauyan El-Rufai ya bayyana cewa har yanzu ba a kai masa takardar kara ba, kuma ya nemi izinin kotu na yin amfani da wata hanya ta daban domin kai masa.
Sai dai mai shari’a ta dakatar da shi, tana bukatar ya fayyace sunan alkalin majistaren da aka ambata a cikin karar.
Daga nan lauyan ya amince da gyaran da kotu ta yi masa, sannan ya nemi a dage shari’ar domin gyara matsalar.
Lauyoyin sauran wadanda ake kara, ciki har da na Sufeto Janar na ‘yan sanda da kuma Babban Lauyan gwamnatin tarayya, ba su yi adawa da bukatar ba.
Daga bisani kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 31 ga Maris domin sauraron sauran bukatun da ke gaban kotu, tare da umartar a fitar da takardar sanarwar sauraro ga wanda ake kara na biyu.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya nuna cewa El-Rufai na neman diyyar Naira Biliyan 1 daga ICPC, alkalin majistare na Abuja, Sufeto Janar na ‘yan sanda da kuma Babban Lauyan gwamnatin tarayya.
A cikin karar da ya shigar, El-Rufai ya bukaci kotu ta bayyana cewa samamen da aka kai gidansa da binciken da aka yi masa a ranar 19 ga Fabrairu ya saba wa hakkokinsa na asali, ciki har da mutunci, ‘yanci, adalci da kuma sirri.
Ya kuma bukaci kotu ta hana amfani da duk wata shaida da aka samu daga wannan bincike tare da umartar a dawo masa da dukkan kayayyakin da aka kwace masa.
ICPC da ‘yan sanda sun mayar da martani cewa sun gudanar da binciken ne bisa sahihin umarnin kotu, tare da bukatar a yi watsi da karar gaba daya.











































