Rundunar ’yan sanda a babban birnin tarayya ta kama wasu mutane bakwai bayan rikici da ya faru a hedikwatar ƙungiyar direbobin mota ta ƙasa NURTW da ke Abuja.
Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sanda a babban birnin tarayya, Josephine Adeh, ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin a Abuja.
Inda ta ce bidiyoyin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke zargin cewa ’yan sanda sun harbe mambobin NURTW ba gaskiya ba ne kuma suna yaudarar jama’a.
Ta ƙara da cewa rundunar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 7:00 na safe a ranar Litinin, inda aka ba da rahoton cewa kimanin mutane 300 sun kutsa cikin hedikwatar NURTW da ke Garki dauke da makamai kamar adda, kwalabe, baka da kibiyoyi, suna kuma kwashe kayayyaki daga wurin.
Ta ce cikin gaggawa, mataimakin kwamishinan ’yan sanda mai kula da ayyuka, Isyaku Sharu, ya jagoranci tawaga zuwa wurin, inda binciken farko ya nuna cewa mutanen na kokarin aiwatar da wani umarnin kotu ba tare da jami’an kotu ko wadanda aka ba izini ba.
Ta bayyana cewa lamarin ya rikide zuwa rikici bayan wasu mambobin NURTW sun bijire wa wannan yunkuri, wanda hakan ya haddasa arangama tsakanin bangarorin biyu.
A cewarta, wani mamba na ƙungiyar ya samu mummunan rauni a wuya sakamakon sara da adda, inda aka ceto shi tare da kai wasu da suka samu raunuka daban-daban zuwa asibiti domin jinya.
Ta kara da cewa an kama mutanen Bakwai a wurin da lamarin ya faru, kuma an gurfanar da su a kotun majistare ta 1 da ke Wuse Zone 2, yayin da zaman lafiya ya dawo yankin.
Ta kuma jaddada kudurin rundunar wajen tabbatar da tsaro da lafiyar duk mazauna babban birnin tarayya.












































