Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma CITAD ta yi kakkausar suka kan cin zarafin ɗan jarida mai ɗaukar rahoto a gidan rediyon Albarka, Mohammed Adamu, da wasu ‘yan sanda suka yi masa yayin da yake gudanar da aikinsa a lokacin bikin Hawan sallah a Bununu, ƙaramar hukumar Tafawa Balewa.
Adamu yana wajen taron ne domin yin rahoto ga kafar yaɗa labarai lokacin da ‘yan sanda karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda na yanki Jamilu Kabir suka tare shi.
Duk da ya bayyana kansa a matsayin ɗan jarida kuma ya yi ƙoƙarin shiga yankin da aka ware wa ‘yan jarida, an zarge su da dukan sa da jami’ai da dama suka yi masa, lamarin da ya jawo masa raunuka a kai har ya nemi kulawar asibiti.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan zartarwa na CITAD, YZ Ya’u, ya sanya wa hannu ranar Litinin a Kano.
CITAD ta bayyana wannan lamari a matsayin babban take hakkin ‘yancin ‘yan jarida da kuma kai hari kai tsaye kan haƙƙoƙinsu a Najeriya.
Ta ce ‘yan jarida na taka muhimmiyar rawa wajen sanar da jama’a da tabbatar da gaskiya, kuma duk wani yunƙuri na tsoratar da su ko cutar da su na raunana dimokuraɗiyya da bin doka.
Ta kuma nuna cewa wannan lamari ba na daban ba ne, domin yana nuna yadda ake ci gaba da muzgunawa da kuma cin zarafin ‘yan jarida daga jami’an tsaro, wanda ke haifar da yanayi na tsoro da kuma takaita ‘yancin kafafen yaɗa labarai wajen gudanar da aikinsu cikin ‘yanci.
Saboda haka, CITAD ta buƙaci a gudanar da cikakken bincike mai gaskiya cikin gaggawa kan lamarin, a gano dukkan jami’an da suka da hannu tare da gurfanar da su a gaban kotu, a kuma biya diyya tare da ba da kariya ga ɗan jaridar da aka ci zarafi, sannan a bayar da umarni da horaswa ga jami’an tsaro domin su mutunta da kare ‘yan jarida yayin aikinsu.
CITAD ta kuma buƙaci Babban sufeton ‘yan sanda da sauran hukumomi su ɗauki mataki mai tsauri domin kawo ƙarshen yawaitar hare-hare kan ‘yan jarida tare da tabbatar da ɗaukar alhaki ga duk masu karya doka.
Ta kuma jaddada cewa Najeriya dole ta ci gaba da kasancewa ƙasa inda ‘yan jarida za su iya gudanar da aikinsu ba tare da tsoro ko barazana ba.













































