Shugabar Hukumar Kula da ingancin abinci da magunguna ta Kasa Farfesa Mojisola Adeyeye ta musanta tallace tallacen daukar ma’aikata da wasu ‘yan damfara ke yadawa da sunanta a shafukan sada zumunta.
Adeyeye a wani taron manema labarai ta bayyana cewa hankalinta ya karkata ne kan yadda wasu ‘yan damfara ke ta yi a shafukanta na sada zumunta, Facebook da Linkedln.
Ta ce masu damfarar da keyiwa mutune alkawarin yi mata aiki da sunan ta, suna neman kudi ne tareda yi musu romon kunne da sauran ababen more rayuwa.
“Sakamakon haka, ba za a ci gaba da amfani da shafin Darakta Janar na dandalin sada zumunta ba har sai illa-masha Allah.
“Ya kamata jama’a su kai rahoto ga hukumar EFCC ta kan lamba +2348093322644, DSS akan lamba +2349153391309.
Shugabar ta NAFDAC ya kuma ce hukumar ba ta amince da duk wani magani da zai iya magance ciwon suga ba sabanin bayanan da gwamnati ta amince da wasu.
A cewarta, idan har akwai wanda aka amince da shi, hukumar za ta sanar da ‘yan Najeriya game da sahihancin lamarin.
Shugabar daganan ta kuma ce hukumar ta kara kaimi wajen yin taka-tsan-tsan a shafukanta na sada zumunta na intanet, musamman kan sanya ido kan irin man shafawa da ta ce ana tallatawa a yanar gizo.













































