PDP ɓangaren jagorancin Turaki ya ki amincewa da hukuncin kotun daukaka kara, zai tafi kotun koli

Kabir Tanimu Turaki

Kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Kabiru Turaki ya ki amincewa da hukuncin kotun daukaka kara wanda ya soke babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba 2025 a Ibadan da ke jihar Oyo.

Mai magana da yawun bangaren Turaki, Ini Ememobong, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa an umurci lauyoyin jam’iyyar da su kalubalanci hukuncin a gaban kotun koli.

Sanarwar ta bayyana cewa bangaren jam’iyyar na ganin cewa aiwatar da wannan hukunci zai haifar da babbar wahala ga mambobin jam’iyyar.

Ya bayyana cewa aiwatar da hukuncin ba tare da wata shakka ba zai jefa mambobin jam’iyyar cikin wahala mai tsanani.

Sanarwar ta kara da cewa domin kauce wa hakan, yayin da ake tuntubar manyan sassan jam’iyyar kan matakin da za a dauka, an umurci lauyoyin jam’iyyar da su gaggauta daukar matakan shari’a domin daukaka kara zuwa kotun koli wadda ita ce kotun karshe a kasar domin yanke hukunci na karshe kan lamarin.

Bangaren jam’iyyar ya bayyana fatan cewa kotun koli za ta gaggauta warware rikicin domin amfanin dimokuradiyya.

Sanarwar ta kuma bukaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai, tare da tabbatar musu cewa rikicin shari’ar zai warware nan gaba kadan.

Ta kara da cewa dole ne a kubutar da jam’iyyar PDP daga hannun wadanda ke nuna kansu a matsayin shugabannin adawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here