Jakadan Nigeria dake Sudan Safiu Olaniyan yace suna jiran takardar shaida daga hukumar Tallafawa al’umna Da kuma NEMA, tare da gwannatin Nigeria dana Cairo kafin abar bakin iyaka da motocin da daliban suke ciki.
Mr Olaniyan ya bayyana haka a wani sakon murya da ya turawa Kungiyar (NIDCOM), ya ce har yanzu suna jiran takardar shaida ne kafin a wuce da motocin daga bakin iyakar Sudan zuwa Egypt.
Ya kuma kara da cewa ofishin jakadancin bashi da hurimin samar da motocin har sai Sunbi doka da kuma jiran Umarnin hukumar NEMA.
Jakadan ya kara jaddadawa iyaye dasu kansu dalibai cewa ma’aikatan ofishin sa dashi kansa sunanan a Sudan har sai sun tabbatar da an kwashe gaba daya daliban dake Sudan, san ya ja hankalin daliban da su kasance cikin natsuwa.













































