Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta tabbatar da Abubakar a matsayin Kwamishinan INEC, Yusuf a matsayin Shugaban NAHCON

Senate 1 750x430

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya roƙi Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin tsohuwar Babbar Jami’ar Rundunar Ruwa, Jamila Abubakar Sadiq mai ritaya, a matsayin Kwamishina mai wakiltar Jihar Adamawa a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC.

Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa buƙatar Tinubu na ƙunshe ne cikin wasiƙa da ya aikewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wadda aka karanta a zauren majalisar a ranar Talata.

A cewar wasiƙar, bukatar na cikin tanadin sashe na 154, ƙaramar sashe na 1 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa gyara.

Tinubu ta cikin wasikar yayi fatan Majalisar Dattawa za ta duba tare da tabbatar da naɗin cikin gaggawa.

Daga bisani, Akpabio ya miƙa buƙatar ga Kwamitin Majalisar Dattawa kan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa domin ƙarin nazarin dokoki da kuma dawowa da rahoto a zauren majalisa cikin mako guda.

Hakazalika, a wata wasiƙa ta daban, Tinubu ya kuma roƙi Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Ambasada Ismail Yusuf a matsayin Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa.

Tinubu ya ce buƙatar tabbatar da naɗin ta yi daidai da tanadin sashe na 3, ƙaramar sashe na 2 na Dokar Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta shekarar 2026, kuma an miƙa buƙatar ga Kwamitin Majalisar Dattawa kan Dokoki da Harkokin Zauren Majalisa domin ƙarin nazari da kuma dawowa da rahoto a zauren majalisa cikin mako guda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here