
Rahotanni daga ƙasar Saudi Arabia sun tabbatar da cewa an ga jinjirin watan Ramadan domin fara watan mai alfarma.
A cewar Haramain, wata kafar yaɗa labarai da ke Saudiyya, bayan ganin jinjirin watan, hukumomin ƙasar za su ayyana ranar Laraba 18 ga Fabrairu 2026 a matsayin ranar farko ta watan Ramadan.
Tun da farko an sanar cewa za a gudanar da duban jinjirin watan a Hawtat Sudair da kuma Tumair a gundumar Al-Majma’ah.
Abdulaziz Al-Muainaa daga cibiyar lura da wata ta Al Hareeq ya ce, “Rana za ta fāɗi daidai ƙarfe 5:52 na yamma, kuma yanayin sararin samaniya ya dace domin ganin jinjirin watan Ramadan.”
Da yake sanar da ganin jinjirin watan a ranar Talata, Haramain ya ce, “An ga jinjirin watan a Saudiyya. Saboda haka, Ramadan 1447 zai fara daga daren yau.
A halin yanzu, Musulmi a Najeriya za su jira sanarwa kan fara Ramadan daga Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Amirul Muminina, Muhammad Sa’ad Abubakar na uku.
Ramadan shi ne wata na tara a kalandar Musulunci kuma mafi tsarki a shekara.
Ana tunawa da saukar da Alƙur’ani ga Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) a cikin sa ne ake dacewa da Lailatul Qadri, wadda ake yi a cikin kwanaki goma na ƙarshe na watan Ramadan.












































