Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce gwamnatinsa har yanzu ba ta samu kowanne irin tallafi daga Gwamnatin Tarayya ba saboda shi ba mamba ba ne na jam’iyyar APC.
Da yake magana a wata hira da DW Hausa, Lawal ya yi iƙirarin cewa wasu jihohi sun samu sama da Naira Biliyan 500 daga Gwamnatin Tarayya a matsayin tallafi, ya ƙara da cewa Zamfara har yanzu ba ta samu komai ba.
Ya ce gwamnatinsa ba ta karɓi rance ba kuma tana amfani da albarkatun da ake da su wajen biyan albashin ma’aikata da kuma aiwatar da ayyukan raya ƙasa.
Ya ce yana ganin hakan ne saboda ba ya cikin APC, yana mai cewa shi mamba ne na PDP, jam’iyyar adawa, kuma ba sa tallafa wa irin su.
Ya ce duk da haka hakan bai hana su aiwatar da wasu ayyukan raya ƙasa a Zamfara ba.
A cewar sa, ba sa karɓar rance, suna amfani da abin da suke da shi wajen biyan albashi, ƙara albashin ma’aikata da kuma biyan masu fansho.
Dare, ya kuma ce, ba su karɓi wani rance ba har yanzu a Jihar Zamfara, kuma suna biyan basussukan da suka rage daga gwamnatin da ta gabata, musamman yadda ake cire Naira Biliyan 1.2 duk wata daga cikin kuɗin jihar domin biyan bashin da aka gada, inda ya ce a baya ana cire naira biliyan 1.5 kafin a rage zuwa Naira Biliyan 1.2.
Gwamnan ya ce bai ji daɗin sauya sheƙar da aka yi kwanan nan daga PDP zuwa APC ba, a don haka shi ba zai bar PDP ba duk da rikicin cikin gida.
Ya ƙara da cewa idan ba zai iya tsayawa takarar zaɓen 2027 a PDP ba, zai nemi wata jam’iyyar siyasa saboda tsarin zaɓen ƙasar ba ya amincewa da ’yan takara masu zaman kansu.













































