Ba mu da wani shiri na tsige mataimakin gwamna — Majalisar dokokin jihar Kano

Aminu Abdulsalam Gwarzo

Majalisar dokokin jihar Kano ta ƙaryata rahotannin da ke ikirarin cewa tana da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam-Gwarzo.

Majalisar ta bayyana cewa irin waɗannan rahotanni ba su da tushe, kuma suna ruɗar da jama’a ba tare da hujja ba.

Majalisar ta ce, babu wata manufa ko yunƙuri da ke gudana a halin yanzu da nufin tsige mataimakin gwamnan.

Ta bayyana cewa labaran da ke yawo a kafafen yaɗa labarai suna da nufin tayar da hankalin jama’a da haifar da tashin hankali a cikin jihar.

Da yake yiwa manema labarai karin bayani, mai magana da yawun shugaban majalisar Kamaluddeen Shawai, ya nuna cewa babu wani kudiri ko shiri a cikin majalisar da ke nufin cire mataimakin gwamnan daga muƙaminsa.

Shawai ya bayyana cewa mataimakin gwamnan na ci gaba da gudanar da aikinsa yadda ya kamata tare da cikakken goyon bayan majalisar dokokin jihar Kano.

Ya buƙaci jama’a da kafafen yaɗa labarai da su yi taka-tsantsan wajen karɓa da yaɗa bayanai ba tare da tantance sahihancinsu ba.

Ya ƙara da cewa sahihin rahoto yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da kwanciyar hankali da daidaiton siyasa a jihar Kano.

Ya jaddada cewa majalisar ba ta mayar da hankali kan jita-jita ko raɗe-raɗin siyasa.

A cewarsa, babban abin da ya sa gaba shi ne yin dokoki masu amfani da kuma sa ido kan ayyukan gwamnati domin bauta wa al’ummar jihar Kano yadda ya kamata.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here