Hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo ta ciro gawar wani mutum mai kimanin shekaru 45 da ya mutu a cikin wata rijiya mai zurfi yayin da yake ƙoƙarin ceto wata akuya a yankin Mokola da ke cikin al’ummar Saki.
Shugaban hukumar, Moroof Akinwande, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a birnin Ibadan, inda ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa game da faruwar lamarin ta wayar tarho daga Yusuf Ismail.
A cewarsa, jami’an hukumar kashe gobara ƙarƙashin jagorancin Kolade Taiwo sun garzaya wurin da lamarin ya faru ba tare da ɓata lokaci ba bayan samun kiran.
Da isowarsu wurin, sun tarar da mutumin mai kimanin shekaru 45 a makale a cikin rijiya mai zurfi.
Jami’an sun ɗauki matakan ceto shi cikin gaggawa tare da amfani da kayan aikin da suka dace, inda suka gudanar da aikin ceto kafin daga bisani su ciro gawar mutumin daga cikin rijiyar.
Akinwande ya bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da mutumin ya shiga rijiyar da nufin ceto akuyar da ta faɗa ciki ta makale, yana mai jajanta wa iyalan mamacin tare da jan hankalin jama’a da su guji shiga rijiyoyi saboda hatsarin da ke tattare da hakan, wanda zai iya haddasa raunuka ko rasa rayuka.
NAN













































