Tinubu zai kai ziyarar aiki jihohin Borno, Bauchi da Lagos

Tinubu depart US 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu zai bar Abuja a ranar Asabar domin kai ziyarar aiki zuwa jihohin Borno, Bauchi da Lagos.

Ziyarar na daga cikin shirye-shiryen aikin gwamnati da kuma wasu muhimman lamurra na ƙasa.

A jihar Borno, ana sa ran shugaban ƙasa zai ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Babagana Zulum ta aiwatar tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya.

Ayyukan sun shafi muhimman sassa da ake ganin sun taka rawa wajen bunƙasa ci gaba da walwalar al’umma a jihar.

Haka kuma, shugaban ƙasa zai halarci bikin aure na Sadeeq Sheriff, ɗan tsohon gwamnan jihar Borno kuma sanata Ali Modu Sheriff, da amaryarsa Hadiza Kam Salem.

Daga Maiduguri, Bola Tinubu zai wuce jihar Bauchi domin jajantawa gwamnatin jihar da iyalan Sheikh Dahiru Bauchi.

Sheikh Dahiru Bauchi ya kasance fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran ɗariƙar Tijjaniyya, wanda ya rasu a ranar 27 ga Nuwamba.

Bayan kammala ziyarar ta’aziyya a Bauchi, shugaban ƙasa zai tafi jihar Lagos inda zai yi hutun ƙarshen shekara.

A yayin zamansa a Lagos, ana sa ran Bola Tinubu zai kasance baƙo na musamman a bikin gargajiya na Eyo da za a gudanar a ranar 27 ga Disamba a filin Tafawa Balewa Square.

Bikin zai karrama fitattun mutane da suka hada da mahaifiyar shugaban ƙasa marigayiya Alhaja Abibatu Mogaji, tsohon gwamnan jihar Lagos Alhaji Lateef Jakande, da kuma Cif Michael Otedola.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here