DIG wanda ya jagoranci kwamitin binciken Abba Kyari, ya fadi ya mutu a Abuja

2E7FCB46 53DF 4350 98F3 5C6B9B28C54C
2E7FCB46 53DF 4350 98F3 5C6B9B28C54C

Joseph Egbunike, mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya mai kula da sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan Najeriya (FCID), ya rasu.

An ce Egbunike ya fadi ya mutu ne a daren ranar Talata bayan ya rufta a ofishinsa da ke hedikwatar rundunar Louis Edet House da ke Abuja.
Ya kasance shugaban kwamitin bincike na musamman (SIP), wanda babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba ya kafa domin binciken Abba Kyari, wanda aka dakatar da shugaban hukumar ‘yan sandan farin kaya (IRT) kan mu’amalar da ya yi da dan damfara na kasa da kasa, Ramon Olorunwa. Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Ya jagoranci sashen binciken manyan laifuka da leken asiri (FCIID) na rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Babban jami’in dan sandan ya yi digirin farko na Kimiyya (Hons) Accounting a Jami’ar Najeriya da ke Nsukka, haka kuma ya yi digirin digirgir (LLB Hons. ), BL, da Masters in International Law and Diplomacy (MILD), da kuma PhD a cikin Criminology.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here