Kungiyar lauyoyi ta ƙasa NBA reshen Kano ta nuna tsananin damuwa kan yadda halin tauye haƙƙin ɗan adam ke ƙara tabarbarewa a jihar, tana mai cewa babu wani ingantaccen ci gaba idan aka kwatanta da bara.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar Usman Umar Fari ya fitar, ta bayyana cewa barazana ga lauyoyi na ƙaruwa yayin da suke gudanar da aikinsu, abin da ya haifar da yawaitar shigar da koke-koken karya haƙƙi a babbar kotun jihar Kano da kotun tarayya da hukumar kare haƙƙin ɗan adam.
Sanarwar ta nuna cewa dubban koke-koke na tauye haƙƙi an shigar da su a babbar kotun jiha kaɗai, tare da wasu kararraki a sauran kotuna.
Lauyoyi da ya kamata su kasance garkuwa ga kare haƙƙi su ma ba su tsira ba, domin da dama an ci zarafinsu ko an tsare su ba bisa ka’ida ba yayin da suke kare kansu ko wasu.
Karanta: hallara yayin da BIKOBA ke gudanar da babban taron ta na shekara karo na 41
Daga cikin misalan akwai kama lauya Mohammad Bashir Adam a ranar 19 ga Satumba 2025 a Abuja, inda jami’an tsaro suka tsare shi a gaban abokan hulɗarsa duk da gabatar da katin shaidarsa, inda daga baya suka amince cewa kuskuren gane mutum ne ya jawo hakan.
Hakanan ranar 22 ga Satumba 2025 jami’an cibiyar yaki da laifukan internet suka kama Uba Sani Hamza a kotun Norman’s Land saboda sunansa ya yi kama da wanda ake zargi da cin mutuncin jami’an gwamnati a dandalin sada zumunta.
A ranar 4 ga Nuwamba 2025 lauya Hamisu Abdulwahhab ya gamu da tsarewa na ɗan lokaci daga ofishin mataimakin babban sufeton ‘yan sanda a Kano kan wani lamari na farar hula.
Sai kuma a ranar 5 ga Disamba 2025 wani gungun jami’ai na musamman daga Abuja suka mamaye ofishin lauya Muhuyi Magaji Rimingado ta hanyar danniya, inda suka yi barazanar harbi ga duk mai tsoma baki, duk da cewa aikinsa kawai shi ne shigar da ƙara bisa izinin babban lauyan jihar.
Sanarwar ta kara nuna damuwa kan yadda rashin tsaro ke ƙaruwa a wasu yankuna na jihar Kano, inda wasu kungiyoyi ke kai hare-hare, kashe mutane da sace su.
Ta kuma bayyana cewa Kano a da na daga cikin wuraren da ake ganin lafiya, amma yanzu halin da ake ciki abin damuwa ne kuma ya kamata a yi Allah wadai da shi.
Kungiyar NBA ta bukaci hukumomi da su dauki mataki cikin gaggawa domin kare haƙƙin jama’a da hukunta masu take doka, tana mai jaddada cewa a ƙarƙashin tsarin dimokuradiyya bai kamata a ci gaba da tauye haƙƙin ɗan adam ba tare da hukunci ba.
Ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya su haɗa kai domin ganin an hana duk wata irin danniya a ƙasar.










































