Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana gudanar da wani taron gaggawa na sirri tare da manyan hafsoshin tsaro a fadarsa da ke Abuja.
Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ce ta tabbatar da hakan a ranar Lahadi.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Babban Hafsan Tsaron Ƙasa (CDS), Janar Olufemi Oluyode; Babban Hafsan Sojojin Sama, Air Vice Marshal Kelvin Aneke; Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Rear Admiral Idi Abbas; Babban Hafsan Bincike na Tsaro, Major General EAP Undiendeye, da Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Major General Waidi Shaibu.
Haka kuma, Babban Sufeton ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, da Daraktan Janar na Hukumar Tsaron farin kaya ta Ƙasa (DSS), Tosin Ajayi, sun halarci taron.
Ko da yake babu cikakkun bayanai kan abin da aka tattauna a taron, sai dai ana kyautata zaton cewa taron na da alaka da jerin rahotannin garkuwa da mutane da aka yi a wasu jihohin arewacin ƙasar.













































