Gwamnan Babban Bankin ƙasa CBN, Olayemi Cardoso, ne zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron shekara-shekara na Bankin Duniya da Asusun Lamunin Kudi na Duniya (IMF) na shekarar 2025, wanda zai gudana a birnin Washington, D.C., daga ranar 13 ga Oktoba.
Cardoso, wanda ke matsayin mataimakin gwamnan Najeriya a cibiyoyin Bretton Woods, zai wakilci Ministan Kudi, Wale Edun, wanda ke rashin lafiya a halin yanzu. Wannan bayani ya fito ne daga sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi a birnin Abuja.
Haka kuma, a cikin tawagar akwai karamin ministan kudi, Doris Uzoka-Anite, tare da wasu manyan jami’an gwamnati.
Wannan na nuna jajircewar Najeriya wajen halartar tarurruka masu muhimmanci da suka shafi tattalin arzikin duniya.
Rahoton Bankin Duniya ya bayyana cewa, muhimman zaman taron sun haɗa da babban zaman kwamitin ci gaba da za a gudanar a ranar 16 ga Oktoba, da kuma taron kwamitin kasa da kasa na Asusun Lamunin Kudi na Duniya a ranar 17 ga Oktoba.
Haka kuma, akwai wasu taruka na musamman da za su shafi tattaunawa kan ci gaban kasashe, tattalin arzikin duniya, da harkokin kasuwanni na kudi, ciki har da tarukan manema labarai da bitoci na manufofin kudi.
NAN












































