Ma’aikatan Jiyya, Ungozoma Sun Fara Yajin Aikin Gargadi Na Kwana Bakwai

nurses

Kungiayar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa – Sashen kula da lafiya ta tarayya (NANNM-FHI) sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai a yau, duk da rokon da gwamnatin tarayya ta yi.

Kungiyar ta ce matakin wanda ya fara da tsakar dare, ya zama dole ne biyo bayan cikar wa’adin kwanaki 15 da ta bayar a ranar 14 ga Yuli, 2025, na neman a inganta walwala, alawus alawus, da kyautata yanayin aiki ga ma’aikatan jinya a fadin cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya.

Shugaban NANNM-FHI na kasa, Morakinyo Rilwan, a ranar Talata, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta gaza yin hulda mai ma’ana da kungiyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here