Sarkin Jama’are ya rasu

DF3E8C1C 6BE2 443E 8870 DA1E58393563
DF3E8C1C 6BE2 443E 8870 DA1E58393563

Allah ya yi wa Sarkin Jama’are na Jihar Bauchi Alhaji Muhammadu Wabi III rasuwa.

Shugaban karamar hukumar Jama’are, Alhaji Sama’ila Yusuf-Jarma, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, rasuwar ranar Lahadi a Bauchi.

Yusuf-Jarma ya ce Wabi, sarkin mai shekaru 92, ya rasu ne da misalin karfe 12:15 na safiyar Lahadi a asibitin koyarwa na Aminu Kano bayan doguwar rashin lafiya.

An nada Wabi sarki ne a shekarar 1970 bayan rasuwar mahaifinsa Muhammadu Wabi II.

Ya rasu ya bar mata hudu da ‘ya’ya 35 da kuma jikoki da dama.

Za a yi jana’izar marigayi sarki a yau da karfe 2:00 na rana. a garin Jama’are.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here