Kungiyoyin kwadago a ranar Talata sun sanar da dakatar da zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar a ranar 27 ga watan Janairu, saboda shirin gwamnati na cire tallafin man fetur.
Shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Ayuba Wabba ne ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a dakin taro na Labour House da ke Abuja.
Ya ce matakin dakatar da zanga-zangar ya biyo bayan sanar da fasa cire tallafin da gwamnatin tarayya ta yi.
Ya ce majalisar zartaswar kungiyoyin kwadago ta Najeriya sun yi taro a safiyar yau (Talata) domin duba sabon matsayin gwamnati kan batun.
“Hukumar gudanarwar bayan zazzafar muhawara ta yanke shawarar dakatar da zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar a ranar 27 ga watan Janairu, 2022 da kuma zanga-zangar kasa da aka shirya gudanarwa ranar 2 ga Fabrairu, 2022.”









































