Jam’iyyar NNPP ta zabi sabon shugabanta na kasa da sauran muƙamai

NNPP

An zaɓi Dr Agbo Major a matsayin sabon shugaban jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na kasa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa taron wanda ya gudana a otal din RockView da ke Apapa a ranar Talata ya samu halartar wakilai da jami’an jam’iyyar a matakin kasa da jihohi.

NAN ta ruwaito cewa sauran zababbun jami’an sun hada da Oginni Olaposi sakataren jam’iyyar na kasa, sai Cif Felix Chukwurah mataimakin shugaban kasa (kudu), Mista Adetoyese Omokanye, ma’ajin kasa, Alhaji Babayo Muhammed mataimakin shugaban kasa (Arewa) da Abdulrasaq Abdulsallam a matsayin sakataren yada labarai na kasa.

Wakilan sun kuma zabi Hajiya Aisha Kade a matsayin shugabar mata ta kasa, Cif Edward Ofomona, shugaban matasa na kasa da Omolara Johnson a matsayin sakatariyar kungiyar ta kasa da dai sauransu.

Labari mai alaƙa: Obasanjo ya soki NNPCL kan gayyatar da ta mai zuwa matatar mai ta Fatakwal

Wadanda suka halarci taron sun hada da mambobin kwamitin amintattu na jam’iyyar (BoT) da kwamitin ayyuka na kasa (NEC) da dukkan masu rike da mukamai na jam’iyyar a kasa baki daya.

NAN ta ruwaito cewa taron wanda ya fara da karfe 9 na dare, ya kare da misalin karfe 4 na safiyar yau Laraba.

NAN ta ruwaito cewa babbar kotun jihar Abia a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2024, a wani hukunci, ta umurci NNPP BoT karkashin jagorancin wanda ya kafa kuma shugaban BoT, Dr Boniface Aniebonam da su fara sake fasalin jam’iyyar tare da sake fasalin dukkan sassan jam’iyyar tun daga gundumomi zuwa babban taron kasa.

Haka kuma kotun ta umurci INEC da ta amince tare da yin mu’amala da sabuwar jam’iyyar ta NNPP.

Aniebonam ya shaida wa mambobin su cewa, bisa ga hukuncin da kotun ta yanke, hukumar ta yi nasarar sauya mukami tare da sake kafa hukumar zartaswar gunduma da har zuwa jami’an shiyya.

A jawabinsa na maraba, Sakataren BOT, Alhaji Mohammed Babayo, ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da kasancewa a dunkule tare da mai da hankali kan manufofinta na samar da sahihin shugabanci da gudanar da mulki wanda zai fifita bukatun ‘yan Nijeriya.

Ya kuma bukaci sabbin zababbun shugabannin jam’iyyar da su jagoranci jam’iyyar da himma da rikon amana da kwazo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here