Majalisar Dattawa Ta Amince da Kasafin Kudi na shekarar 2022

E978AFD1 79AC 4FA9 B790 9CED90444BAD
E978AFD1 79AC 4FA9 B790 9CED90444BAD

Majalisar dattijai a zamanta na yau laraba amince da kasafin kudi na shekarar 2022 wanda ya haura tiriliyan  naira 17.126.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mikawa majalisar dokokin kasar kasafin kudi naira tiriliyan 16.391, ina majalisar ta kara shi zuwa 17.126.

Majalisar dattawan ta kuma daga darajar man fetur zuwa dala 62 sabanin dala 52 da bangaren zartarwa ya gabatar, yayin da aka ajiye kudin a kan N410.15.

Ta ce an samu karin farashin man ne domin a nuna darajar ganga mai a kasuwannin duniya a halin yanzu.

A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin kasafin kudi Jibrin Barau ya ce sai da majalisar ta yi duba na tsanaki tare da tsefe kasafin kafin ta amince dashi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here