Jihar Kwara: Gwamna Abdulrazaq ya kafa sabon majalisar gudanarwar KWASU

gwamna, Jihar kwara, sabuwar, majalisar
Gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ya nada sabuwar majalisar gudanarwa na jami’ar jihar Kwara KWASU.Wata sanarwa da babban Sakataren Yada Labarai na...

Gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ya nada sabuwar majalisar gudanarwa na jami’ar jihar Kwara KWASU.

Wata sanarwa da babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Rafiu Ajakaye ya fitar a ranar Laraba, ta ce tsohon Mataimakin Shugaban Jami’ar Ilorin Farfesa Abdul Ganiyu Ambali ne Shugaban Majalisar, wanda ke da wasu 5 a matsayin mambobi.

Karanta wannan: Saudiya zata bada damar sayar da Barasa ga wadanda ba Musulmi ba

SOLACEBASE ta rawaito cewa sauran mambobin su ne Farfesa Ibrahim Jawondo da Farfesa Aishetu Abdulkadir da Barista Teju Oguntoye da Abdullahi Biogera da Daudu Funmilayo Maryam (mai masaukin baki da kuma mazabar matasa).

Sanarwar tace nadin ya fara aiki ne nan take.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here