Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa domin halartar taron baje kolin duniya wato EXPO na shekarar 2020.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa Jakadan UAE a Najeriya, Dr Fahad Obaid Al Taffa ne ya tarbi Buhari.

A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, taron EXPO, mai taken, “Haɗa tunani, Samar da makoma”, ya samar da dana ga Najeriya ta shiga cikin kasashe sama da 190 don yin haɗin gwiwa mai ma’ana don kyautata goben al’umma.
Sanarwar ta ce taron na Expo 2020 da za a yi a Dubai, wanda coronavirus ta haifar da tsaiko a makon da ya gabata, an fara shi ne a watan Satumba kuma shi ne bikin baje kolin duniya na farko a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ake sa ran zai kwashe kwanaki 182 ana yi.

Ya kara da cewa shugaban zai samu rakiyar ministoci da suka hada da Geoffrey Onyeama, ministan harkokin waje; Adeniyi Adebayo, ministan masana’antu, kasuwanci, da zuba jari; Zainab Ahmed, ministar kudi; Bashir Magashi, ministan tsaro; Hadi Sirika, ministan sufurin jiragen sama, da Mohammad Abubakar, ministan noma da raya karkara.

Ana sa ran shugaban zai dawo Najeriya ranar Lahadi 5 ga Disamba, 2021.














































Ya Allah Ina ne man zama lfy a ko da yaushe