Majalisa Ta 10: Sanata Akpabio Ya Sanar da Sabbin Shugabannin Majalisar Dattawa

Senate 1 750x430
Senate 1 750x430

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da waɗanda suka samu nasarar zama jagororin majalisar dattawa ta 10.

Sanata Akpabio ya bayyana cewa an zaɓi sabbin shugabannin ne ta hanyar maslaha.

Sabbin jagororin majalisar sun haɗa da Sanata Opeyemi Bamidele daga jihar Ekiti a matsayin shugaban masu rinjaye da Sanata Dave Umahi daga Ebonyi a matsayin mataimakinsa.

Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya zama babban mai ladaftarwa na majalisa yayin da Sanata Lola Ashiru, ya samu nasarar zama mataimakinsa.

A ɗaya bangaren kuma Sanata Akpabio ya bayyana sabbin shugabanni daga ɓangaren marasa rinjaye. Sun ƙunshi Sanata Simon Davou (Filato ta arewa – PDP) a matsayin sabon shugaban marasa rinjaye yayin da Oyewunmi Olarere (Osun ta yamma – PDP) ya zama mataimakinsa.

Sauran sun haɗa da Sanata Darlington Nwokeocha mai wakiltar jihar Abia ta tsakiya a inuwar LP a matsayin mai ladaftarwan marasa rinjaye da kuma Rufai Hanga (NNPP, Kano ta tsakiya) a matsayin mataimakinsa.

SHARHI 1

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here