Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wakilan Bankin Amurka a Villa 

8666770790895027741
8666770790895027741

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan da ƙara haɓɓaka dangantakar da ke tsakanin ƙasar nan da ƙasashen waje. A ranar Talata, 4 ga watan Yuli, Shugaba Tinubu ya sanya labule da wakilan bankin Amurka a fadar shugaban ƙasa da ke a Aso Rock Villa.

Kamar yadda Legit.ng ta tattaro, wakilan bankin na Amurka sun zo ne a ƙarƙashin jagorancin shugaban bankin na ƙasa na yankin Saharar Afirika, Mr Bernard Mensah.

Sauran manyan ƙusoshin bankin na Amurka da suka halarci zaman sun haɗa da shugabar yankin Saharar Afirika, Mrs Yvonne Ike Fasinro da shugaban fannin zuba jari na yankin Saharar Afirika, Mr Chuba Ezenwa.

Har yanzu dai cikakkun bayani kan tattaunawar ta su basu fito ba, amma alamu masu ƙarfi na nuni da cewa zaman na su zai yi ƙoƙarin samar da hanyoyin da za su taimaka wajen dawo da tattalin arziƙin ƙasar nan akan turba.

Tun bayan dawowarsa daga hutun Sallah da ya yi a birnin Legas, Shugaba Tinubu ƴa duƙufa aiki gadan-gadan wajen tafiyar da mulkin ƙasar nan, inda ya gana da mutane masu ruwa da tsaki a fannoni daban-daban.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here