Yanzu-yanzu: An Dakatar Da Binance Daga Aiki A Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta sanya dokar ta-baci tareda hana ayyukan kamfanin Binance Nigeria Limited a Kasar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takadda da Hukumar Kula da Kasuwanci ta kasa ta fitar.

Hukumar ta umurci Binance da “batare da bata lokaci ba ya daina neman masu zuba jari na Najeriya ta kowacce hanya.”

Sanarwar tana cewa; “Kamfanin Binance Nigeria Limited bashi da rajista kuma ayyukansa a Najeriya sun sabawa doka. Duk wasu masu saka hannun jari da ke hulɗa da shi ka iya tsintar kan sa cikin haɗari.

“An gargadi masu saka hannun jari na Najeriya cewa saka hannun jari a cikin kadarori na Binance crypto yana da matukar hadari kuma yana iya haifar da asarar jarin su gaba daya.

“Hukumar za ta samar da sabbin bayanai game da ƙarin matakan da suka dace game da ayyukan Binance Nigeria Limited, da sauran dandamali iri wannan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here