Wata dalibar jami’ar jihar Yobe, Yobe State University, dake Damaturu, mai suna Maryam Lawan Goroma, ta mutu jim kadan bayan ta gama rubuta jarrabawa.
kamar yadda rahoto ya nuna, ta wadi sumammiya a ranar Alhamis 27 ga watan Apirilu, na wannan shekarar, inda aka garzaya da ita asibiti inda aka tabbatar da rasuwar ta ta.
Abokin karatun ta mai suna Bukar Maisandari, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tana cikin koshin lafiya kafin rasuwar ta ta.
“Innaa Lillaahi Wa Innaa Ilaihir Raaji’uun. yanzu nake samun labarin rasuwar abokiyar karatuna, Maryam Lawan Goroma, wacce har zuwa yamma kafin rasuwar ta tana cikin koshin lafiya, ina addu’ar Allah ya jikanta da rahama ya sa aljannace makomarta, sannan ina mika sakon ta’aziyata zuwa ga yan uwanta tare da abokan karatun mu.” inji shi.
Sadai kuma, wani abokin karatun ta mai suna Abubakar Zaid, ya ce tayi korafin cewa cikin ta yana yi mata ciwo lokacin da suke rubuta jarrabawa.
Tuni dai akai jana’izarta a yau Juma’a a Sabon Fegi, Damaturu.












































