Tinubu ya nada Onanuga, Marwa, da wasu mutane 11 a kwamitin karbar mulki.

Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya sanar da kwamitin mutane 13 na shugaban kasa da ya kunshi fitattun ‘yan Najeriya domin shirya taron rantsar da shugaban kasa da mataimakinsa.

Tinubu, a wata wasika da ya aikewa sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana tsohon Sanata mai wakiltar Borno ta Arewa kuma mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Abubakar Kyari a matsayin kodineta kuma darakta na Kudi da Kasafin Kudi na Kwamitin.

Babban Darakta a bankin Najeriya Export-Import (NEXIM) Bank, Stella Okotete za ta yi aiki a matsayin sakatariya, tsare-tsare da sa ido, yayin da Mista Makinde Araoye, tsohon dan takarar gwamna a APC daga jihar Ekiti zai kasance a matsayin Darektan tsare tsare.

Mai magana da yawun yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Mista Bayo Onanuga, zai kasance shugaban sashen yada labarai da wayar da kan jama’a, yayin da kwamishiniyar lafiya ta jihar Cross Rivers kuma shugabar mata ta jam’iyyar APC ta kasa a halin yanzu, Dokta Betta Edu za ta jagoranci tawagar likitocin da za su jagoranci kwamitin kaddamarwar.

Wani kanin marigayi shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Kanar Abdulazeez ‘Yar’aduwa ne zai rike mukamin shugaban kwamotin tsaro da a bikin rantsar da inda uwargida Zainab Buba Marwa, ita ce zata shirya liyafar cin abinci da kuma daren shagulgulan bikin rantsar da shi.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Samira Saddik, Abuh Andrew Abuh ( masauki), Dr. Danladi Bako (Laccar farko), Hajiya Hadiza Mohammed Kabir (Sufuri), Donald Wokoma da sauran su.

Idan za’a tuna tun farko dai zababben shugaban kasa, Tinubu ya mika sunayen Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi da tsohon kwamishinan kudi na jihar Legas, Mista Wale Edun ga Boss Mustapha domin a saka su a matsayin wakilansa a kwamitin mika mulki.

Ana sa ran za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga Mayu, 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here