Rundunar yan sandan Zamfara ta tabbatar da sace mata daliban jami’a su 2

Nigeria Kidnappings Bandits deputy
Nigeria Kidnappings Bandits deputy

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Kolo Yusuf psc, ya tabbatar wa al’umma musamman iyalai da kuma mahukuntan jami’ar tarayya ta Gusau cewa, ana ci gaba da kokarin kubutar da daliban jami’ar guda biyu da yan ta’adda suka sace su a safiyar yau Lahadi, inda jami’an tsaro na ‘yan sanda suka tsananta bincike don ceto su.

Bayanan da rundunar ta samu sun nuna cewa, da misalin karfe 1:00 na daren wayewar yau Lahadi 2 ga watan Afrilu ne wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai farmaki kauyen sabon gida da ke karamar hukumar Bungudu inda suka shiga gidan kwanan dalibai mata na jami’ar inda suka kulle wasu mutane biyu da ƙwace wayoyinsu tare da sace ɗalibai matan su biyu da ke karatu a sashen Microbiology na jami’ar.

Bayan samun rahoton, tawagar kar ta kwana ta rundunar ‘yan sanda ta isa wurin da lamarin ya faru, sai dai tuni ‘yan bindigar sun  gudu tare da wadanda lamarin ya ritsa da su inda har kawo yanzu ba a gano inda suka buya ba.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kara tura dakarun da za su ci gaba da aikin ceto wadanda aka yi garkuwa da su, tare da cafke wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Don haka kwamishinan ‘yan sandan ya yi kira da a ci gaba da bai wa rundunar goyon baya a kokarin ‘yan sanda na samun nasarar ceto ɗaliban tare da cafke bata garin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here