Kotun Ƙoli ta yi watsi da shari’ar kisan Kudirat da aka Danganta da Al-Mustapha

Hamza Al Mustapha (1)

Kotun Ƙolin Najeriya ta yi watsi da shari’ar kisan gillar marigayiya Alhaja Kudirat Abiola da ake tuhumar Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya) a kai, wanda ya taɓa zama Babban Jami’in Tsaron tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Sani Abacha.

Kotun, ta yi hukuncin ne a yau Alhamis, inda Mai shari’a Uwani Aba-Aji ta jagoranci kwamitin alkalai biyar, ta yanke cewa gwamnatin Jihar Legas ta yi watsi da shari’ar tun bayan samun damar sake buɗe ta a shekarar 2014.

Kotun ta lura cewa tun bayan bayar da umarnin sake buɗe shari’ar, gwamnatin Legas ba ta shigar da sanarwar ɗaukaka ƙara watau notice of appeal ko wata takardar shari’a ba, duk da cewar an ba ta wa’adin kwanaki 30. Haka kuma, babu wani lauya da ya wakilci jihar a zaman kotun.

Lauyan Al-Mustapha, Paul Daudu, SAN, ya shaida wa kotun cewa sama da shekaru tara sun shige ba tare da gwamnatin Legas ta ɗauki wani mataki ba, yana mai roƙon kotun da ta yanke hukuncin cewa an yi watsi da shari’ar gaba ɗaya.

Kotun Ƙoli ta amince da wannan buƙata, inda ta bayyana rashin gamsuwarta da halin ko-in-kula da gwamnatin Legas, tare da jaddada cewa tsawon lokacin da ya shige ya nuna karara cewa jihar ta rasa sha’awar ci gaba da shari’ar.

Sakamakon haka, Kotun ta yi watsi da shari’ar mai lamba SC/CR/45/2014 da SC/CR/6/2014, tare da kawo ƙarshen duk wani yunƙuri na sake buɗe shari’ar kisan Kudirat Abiola, wadda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta wanke Al-Mustapha tun a 12 ga Yuli, 2013.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here