Majalisar dattawan Jami’ar Bayero da ke Kano ta amince da ba da shawarar nada Farfesa Ahmad Muhammad Tsauni, wanda shi ne Daraktan Ma’aikatar Buga Littattafai ta jami’ar, domin zama Mataimakin Shugaban Jami’a mai kula da harkokin karatu.
SolaceBase ta ruwaito cewa an yanke wannan shawara ne a taron majalisar jami’ar karo na 428 da aka gudanar a ranar Alhamis, 2 ga Oktoba, 2025.
Za a mika wannan shawara ga majalisar gudanarwa ta jami’ar domin nazari da amincewa a taronta na gaba.
Wurin Mataimakin Shugaban Jami’a mai kula da harkokin karatu ya zama babu mai rike da shi bayan nada Farfesa Haruna Musa, fsi, a matsayin Shugaban Jami’a na 12.
A yayin taron, majalisar ta kuma zaɓi Farfesa Ummu A. Jalingo a matsayin wakiliyar majalisar dattawa a cikin majalisar gudanarwa ta jami’ar.
Farfesa Ahmad Muhammad Tsauni, wanda ya kware a fannin tattalin arziƙi, ya samu digirin digirgir a wannan fanni daga Jami’ar Bayero, inda ya yi aiki na sama da shekaru ashirin.
Ya fara aikin koyarwa a 2004 a matsayin mataimakin malami, sannan ya zama Farfesa a 2019.
Ya yi aiki a fannoni da dama na gudanarwa da na ilimi a jami’ar, ciki har da shugaban sashen tattalin arziƙi, mataimakin level coordinator da kuma Dean na sashin zamantakewa.
A yanzu haka, yana jagorantar Ma’aikatar Buga Littattafai ta jami’ar, inda yake taka muhimmiyar rawa wajen inganta wallafe-wallafen ilimi da yada bincike.
Farfesa Tsauni ya kuma ba da gudunmawa a matsayin memba a kwamitoci daban-daban a matakan sashen, abin da ya nuna jajircewarsa wajen inganta harkokin karatu da ci gaban jami’a.













































