Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Litinin, ta yi watsi da karar da ke neman kalubalantar cancantar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na yin takarar kujerar shugaban kasa.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Inyang Ekwo, ya yi watsi da karar bisa dalilin cewa wanda ya shigar da karar ba shi da hurumin yin hakan.
Solacebase ta ruwaito cewa wata kungiya, Incorporated Trustees of Egalitarian Mission for Africa (EMA) ce ta maka Atiku, PDP, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) da kuma Babban Lauyan Hukumar gwamnatin tarayya a matsayin wadanda ake tuhuma na 1 zuwa na 4.
Kungiyar ta EMA tana kalubalantar cancantar Atiku na tsayawa takarar shugaban kasa bisa hujjar cewa shi ba dan Najeriya bane ta haihuwa.
NAN ta ruwaito cewa, a ranar 27 ga watan Yuli, 2021, gwamnatin jihar Adamawa, ta hannun babban lauyanta, ta bukaci kotu ta bada umarnin a shiga cikin karar.













































