Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta yi nasarar cafke wasu miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai fiye da naira miliyan 82 a jihar.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Ya ce an samu nasarar ne sakamakon sahihin bayani da aka tattara a ranar 20 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 1:00 na rana.
A cewarsa, jami’an tsaro sun bi wata mota ma ake zargi har zuwa wani gida da ke unguwar Rimin Auzinawa a Kano, bayan samun rahoto cewa tana ɗauke da katunan miyagun kwayoyi.
A nan ne aka kame wani matashi mai shekaru 19 da haihuwa mai suna Usman Umar.
Binciken da aka gudanar a gidan ya haifar da gano fakiti 603 na kwayar Tramadol, wacce ke ɗauke da ƙwayoyi 60,300 da darajarsu ta kai naira miliyan 60.3.
Karanta: PENGASSAN ta dakatar da kai iskar gas zuwa Kamfanin Mai na Dangote
Haka kuma an gano fakiti 299 na kwayar Pregabalin da ke ɗauke da ƙwayoyi 44,850 da kimar su ta kai naira miliyan 22.4.
Jimillar darajar miyagun kwayoyin da aka gano ta kai naira miliyan 82.7, kamar yadda SP Kiyawa ya tabbatar.
Ya ce wanda ake zargi yana taimakawa bincike domin gano sauran masu hannu a cikin wannan haramtacciyar sana’ar.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da gudummawar al’ummar Kano wajen bayar da bayanai da suka kai ga wannan nasara. Ya jaddada cewa hakan ba zai yiwu ba sai da haɗin kai da wayar da kan jama’a.
Bakori ya kuma tabbatar da aniyar rundunar wajen ci gaba da yaƙi da safarar miyagun kwayoyi da amfani da su a Kano, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai cikin sirri domin ƙara tabbatar da zaman lafiya.













































