Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce, ‘yan baya za su yi wa shugabannin kasar nan hukunci da tsauri idan suka bar makarantun gwamnati suka ruguje.
Shettima ya bayyana haka ne a ranar Laraba a wajen taron kaddamar da allunan da kamfanin sadarwa na MTN Nigeria Plc ya rabawa daliban makarantar sakandiren kimiyyar gwamnati da ke Pyakasa, Maitama, Abuja.
Ya ce shugaban kasa Bola Tinubu yana da sha’awar inganta makarantun gwamnati, inda ya ce an tsara shirin bada rancen kudi ga dalibai ne domin baiwa ‘ya’yan talakawa damar samun ilimi.
Karin karatu: Kashim Shatima ya yabawa BUK bisa samar da ingantaccen ilimi da tsarin daukar dalibai
“Wannan makarantar gwamnati ce, ba zato ba tsammani, dukanmu da ke zaune a kan babban tebur duk rainon tsarin makarantun gwamnati ne kuma yan baya za su yi mana hukunci mai tsanani idan muka bar tsarin makarantun gwamnati ya rushe”.
Shettima ya ce “Muna iya samun damar tura namu makarantu masu zaman kansu, amma ‘ya’yan talakawa da muka bar su sun lalace a makarantu marasa inganci za su zarge mu.”
Ya kuma ba da tabbacin cewa tare da hadin gwiwar kungiyoyi irin su MTN, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da yin iya kokarinta don ganin an samar da ingantattun kayan aiki a makarantun gwamnati.
Mataimakin shugaban kasar ya bukaci daliban da su yi amfani da allunan don fadada iliminsu, yana mai cewa “Ku kara kaifin basira, kuma ku shirya kanku don damammakin da ba su da iyaka na gaba.”
(NAN)