Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta yi kira ga gwamnonin jihohin Arewa 19 da su gudanar da wani gagarumin garambawul na mallakar filaye da kuma kula da filaye domin hana baki kwace filayensu.
Kungiyar ta yi Allah wadai da halin da ‘yan Arewa ke ciki na hana su siyan filaye a kudancin kasar nan, duk kuwa da abin da ta kira “Arewa na karbar baki mara iyaka” ga mutanen Kudu da ke zaune da masu gidaje a Arewa.
Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar ACF, Alhaji Bashir Dalhatu, wanda ya tabo batun a yayin wani taro a jihar Kaduna, ya bayyana cewa rashin jituwa da nuna kyama ga ‘yan Arewa mazauna Kudu, ya kara ta’azzara sakamakon rashin daidaito da manufofin gwamnatin tarayya na nuna wariya ga Arewa.
Dalhatu ya ce lokaci ya yi da gwamnoni da ’yan majalisa a jihohin Arewa za su gudanar da wani gagarumin garambawul na tsarin mallakar filaye da kuma kula da su.
karin karatu: Hajjin 2025: NAHCON ta sanar da ranar 9 ga Mayu don fara jigilar maniyyata
Ya yi nuni da cewa bukatar wannan garambawul a bayyane take, musamman ganin yadda ‘yan kasashen waje ke neman filaye a Arewa a halin yanzu.
Zargin Zaluntar ‘Yan Arewa
Taron ya kuma yi zargin cewa ana cin zarafi da kai wa ’yan Arewa hari a yankin Kudancin kasar nan, inda ta bayyana hakan a matsayin abin ban dariya da raɗaɗi, ganin cewa tsawon shekaru aru-aru, Arewa ta buɗe kofofinta da kuma maraba da jama’a daga sassan Nijeriya.
ACF ta kuma bukaci da a gaggauta sake duba dokar kafa babban birnin tarayya ta shekarar 1976, da kuma bukatar a samar da jiha ga ’yan asalin Abuja, wadanda su ne asalin ‘masu mallakin babban birnin tarayya.
A cewar shugaban ACF BOT, dokar da ta kafa babban birnin tarayya Abuja a shekarar 1976 ta bayyana wasu matakai da gwamnatin tarayya za ta dauka a matsayin sharadi na zama a babban birnin tarayya.
Wannan rashin adalci da cin zarafi da ake yiwa ’yan asalin babban birnin tarayya Abuja ya bukaci a sake duba lamarin cikin gaggawa. Ya kara da cewa, lokaci ya yi da Nijeriya za ta cika nauyin da ya rataya a wuyanta ga ’yan asalin Abuja, ciki har da samar da nasu jihar a cikin tarayyar Najeriya.
Dangane da sake barkewar kashe-kashe da hare-hare a wasu jihohin Arewa, kungiyar ACF ta yi kira da a kara yin hadin gwiwa da tuntubar gwamnati da shugabannin gargajiya da na addini domin kawo karshen rikicin.












































