Kungiyar masu masana’antu ka ƙasa (MAN) ta bayyana cewa yawaitar karin kudin wutar lantarki na kawo cikas ga ayyukan masana’antu da kuma ci gaban tattalin arzikin kasa.
Darakta Janar na MAN, Segun Ajayi-Kadir, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Legas.
Ajayi-Kadir ya jaddada cewa wutar lantarki wani muhimmin abu ne a masana’antu, wanda ke tasiri sosai kan kari ko saukar farashin kayayyaki.
Ya jaddada cewa babu wata kasa da za ta iya samun ci gaban masana’antu ba tare da tabbatar da tsaron makamashi ba.
Sabon labari: TUC ta ki amincewa da karin kashi 65% na kudin wutar lantarki
A cewarsa, duk wani karin kudin fito da za a yi zai yi illa ga samar da kayyayaki da kasuwancinsa a Najeriya.
Ya yi gargadin cewa irin wannan zai kara dagula farashin samar da kayayyaki, da kara matsa lamba, da kuma kara rage kudaden shiga na masu amfani da su.
Ajayi-Kadir ya kara da cewa hakan zai kara durkushewar masana’antun, zai lalata ribar da ake samu, tare da kara haifar da rashin aikin yi, da kuma tilasta wa wasu kamfanoni masu zaman kansu rufewa.
“Saboda muhimmiyar rawar da tsaron makamashi ke takawa a cikin masana’antu na Najeriya ya sa aka mayar da bangaren wutar lantarki a matsayin kamfani a shekarar 2013.
“Abin takaici, wannan sayar da hannun jari bai haifar da sakamakon da ake tsammani ba,” in ji shi.
Shugaban ya kara da cewa karfin wutar lantarkin da Najeriya ke da shi ya kai megawatt 10,000.