Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Odu bayan sa hannun shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Majalisar ta
amince da dakatar da shirin ne a ranar Alhamis yayin zaman majalisar da aka koma yi a Fatakwal, babban birnin jihar.
A baya, majalisar ta fara shirin tsige gwamnan da mataimakiyarsa a zamanta na farko na shekarar 2026 bisa zargin aikata manyan laifuka, ciki har da rushe ginin majalisar dokokin jihar da kuma zargin kashe kuɗaɗe ba tare da amincewar majalisa ba, da sauran zarge-zarge.
Za a kawo ƙarin bayani nan gaba.













































