‘Yan bindiga sun kashe farar hula fiye da 100 a gabashin Burkina Faso

Daliban da akayi garkuwa dasu  a Kaduna sun shaki iskar yanci
Daliban da akayi garkuwa dasu  a Kaduna sun shaki iskar yanci

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe farar hula fiye da 100 a hare-hare daban-daban da suka kai ƙauyukan lardin Kompienga da ke gabashin Burkina Faso, kamar yadda kafar yaɗa labarai mai zaman kanta ta yankin ta rawaito.

Rahoton ya ce, an yi kisan kiyashi kan fararen hula na Kpadiari da Nadiagou da Tindangou a ranar 16 ga watan Maris” inda rahoton ya ƙara da cewa an samu labarin mutuwar mutane aƙalla 130.

Karin labari: Hukumar KNUPD ta rusa gidaje a unguwar Gurun Gawa

Masu amfani da intanet sun ce waɗanda abin ya shafa da suka haɗa da mata da ƙananan yara, ana zarginsu da alaƙa da ƙungiyoyin ‘ƴan bindiga.

A baya-bayan nan dai ƙasar Burkina Faso ta sha fama da kashe ɗaruruwan fararen hula da ake zargin wasu ƙungiyoyin ‘ƴan bindiga ne.

Ana kuma zargin jami’an tsaron da aikata kisan gilla kan mutane da dama.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here