Yadda Muka Mallaki Obajana shekaru 20 da suka wuce – Kamfanin Dangote 

3bf0a593520b5e7d
3bf0a593520b5e7d

Shugabannin kamfanin Dangote Industries Limited sun bayyana cewa an bi dokoki wajen sayen filin kamfanin simintin Obajana a shekarar 2002.

This Day tace wannan bayani ya sabawa matsayar gwamnatin jihar Kogi, wanda take cewa an mallaki kamfanin ne ba tare da an bi ka’ida da doka ba. Bugu da kari Dangote Industries Limited yace yana biyan gwamnatin Kogi haraji da duk wasu kudi da suka kamata tun lokacin da suka fara aiki a 2007.

A wani jawabi da kamfanin ya fitar a ranar Talata, 12 ga watan Oktoba 2022 ne ya yi wannan karin haske.

“A 2003, kamfanin Dangote Industries Limited ita kadai ta saye kasar da aka gina kamfanin simintin Obajana, bayan ta saye hannun jarin kamfanin a 2002. An yi hakan ne bayan yarjejeniyar da ta shiga da KSG domin sa hannun jari a jihar Kogi. An ba DIL satifiket uku bayan biyan kudi, kuma aka sallami masu fili.”

Hakan na zuwa ne bayan an samu sabani tsakanin kamfanin da gwamnatin Yahaya Bello. Jawabin ya tabbatar da cewa DIL kadai ya biya kudi ya saye kamfanin, bayan nan ya saye hannun jari a kamfanin simintin Obajana shekaru 20 da suka wuce.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here