Yadda Kwankwaso ya yi maraba da mutanen da suka sauya sheƙa daga APC zuwa NNPP a Kano

NNPP3

Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya danganta karuwar sauya sheka ta siyasa ga fitaccen salon shugabancin jam’iyyar NNPP da kuma jajircewa wajen samar da shugabanci na gari a jihar Kano.

Jagoran tafiyar Kwankwasiyyan, ya bayyana haka ne a ranar Juma’a ta shafin sa na Facebook.

“Jiya wani muhimmin lokaci ne, yayin da na karɓi dubban masu sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa NNPP” in ji shi.

Da ya ke jawabi a wurin taron, ya yi wa waɗanda suka sauya sheƙar alkawarin yin adalci da hadin kai a NNPP.

“Sakamakon salon shugabancinmu da jajircewarmu wajen samar da shugabanci na gari na ci gaba da jawo hankalin ‘yan Najeriya masu kishin kasa a cikin mu, ina kira ga sauran wadanda ke ci gaba da tunanin daukar wannan matakin ba tare da bata lokaci ba,” inji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here