Yadda jami’an NSCDC suka doki wanda ake zargi da laifi har ya mutu a Kano

WhatsApp Image 2026 01 09 at 21.45.03 750x430

Al’ummar yankin Fagge a Jihar Kano sun shiga tashin hankali sakamakon zargin cewa jami’an Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya NSCDC sun doki wani mutum mai suna Khalifa Usman Abdullahi har ya rasu yayin da yake tsare a hannunsu.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a yankin, abin da ya haifar da zanga-zangar mazauna unguwar, inda wasu matasa suka yi barazanar ƙona ofishin NSCDC na yankin, suna neman a yi adalci kan mutuwar marigayin.

Bayanai sun nuna cewa jami’an NSCDC sun zargi Khalifa Usman Abdullahi da satar kuɗin wasu jami’an hukumar.

Sai dai mazauna yankin sun ce maimakon bin ƙa’idojin bincike na doka, an yi masa duka mai tsanani.

Al’ummar yankin sun bayyana cewa an yi wa Khalifa munanan duka da ya jikkata shi ƙwarai, lamarin da ya kai ga mutuwarsa daga baya, abin da ya jefa iyalansa da al’umma cikin jimami da fushi.

Ɗan uwansa babba, Usman Abdullahi, ya bayyana cewa Khalifa ya shafe kusan shekaru biyar yana aiki tare da hukumar tsaron, kuma bai taɓa samun wata matsala ta ladabtarwa ko rikici ba.

Zanga-zangar ta ƙara ɗaukar zafi, inda wasu matasa suka fito tituna suna zargin jami’an da amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba da kuma aikata hukunci ba tare da shari’a ba.

Daga bisani jami’an tsaro suka shiga tsakani domin dawo da zaman lafiya da hana rugujewar doka da oda.

A martaninsu, rundunar NSCDC ta Jihar Kano ta ɗauki matakai na gaggawa yayin da bincike ke gudana.

Kakakin rundunar, mataimakin kwamandan NSCDC Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da cewa an miƙa kwamandan NSCDC na Fagge, CSC Amina Musa Kolawale, tare da sauran jami’an da abin ya shafa ga ’yan sanda domin ci gaba da bincike, tare da cire ta daga muƙaminta tare da naɗa CSC Bashir Isa Abubakar domin kula da rundunar har zuwa kammala binciken.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here