Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NIMET) ta ankarar da wasu mazauna jihohin arewa kan su shirya wa mamakon ruwan sama a ƴan kawa naki masu zuwa.
A cewar sanarwar da aka fitar ranar Alhamis, ana ganin gangamowar hadari a wasu sassan arewacin ƙasar har da Borno da Taraba da Gombe da Bauchi da Kano.
Ana kuma tsammanin hadarin zai yaɗu zuwa yammaci
Sanarwar ta ƙara da cewa hadarin da ake fuskanta ana sa ran zai kai ga gabashin ƙasar haɗe da iska a jihohin Plateau da Nasrawa da Jigawa da Adamaa da Yobe da Borno da Bauchi da Gombe da Kaduna da Kano da Katsina cikin sa’a biyu nan gaba.
NIMET ta ce ga yankunan da ake tsammanin hadari, akwai yiwuwar a yi iska mai ƙarfi za ta gabaci ruwan sama a don haka hakan na iya shafar bishiyoyi da turakun wutar lantarki da gine-gine masu rauni.
Hukumar ta kuma shawarci jama’a su yi taka tsan-tsan su kuma zauna a cikin gida musamman a yayin mamakon ruwan saman.
NIMET ta kuma shawarci kamfanonin jiragen sama da su kasance suna da bayanan yanayi domin tsara tafiye-tafiyensu.













































