Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa (TUC) ta yi Allah-wadai da abin da ta kira “aikata rashin adalci ga ma’aikata” daga hukumar gudanarwar kamfanin sarrafa mai na Dangote, bayan korar wasu ma’aikata bisa zargin amfani da haƙƙinsu na kundin tsarin mulki na ’yancin shiga ƙungiya.
Sakataren Janar na TUC, Comrade N.A. Toro, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa ma’aikatan da aka kora dukkansu mambobi ne na ƙungiyar haɗaɗɗiyar PENGASSAN, inda aka ce an azabtar da su ne saboda bayyana mambobinsu a fili.
Ya bayyana cewa wannan mataki ya sabawa sashe na 40 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka yiwa gyara), wanda ke tabbatar da haƙƙin ’yan ƙasa na yin haɗin kai da shiga ƙungiya.
Haka kuma ya saba wa alkawurran Najeriya a ƙarƙashin yarjejeniyoyin ƙungiyar ƙwadago ta duniya (ILO).
TUC ta yi kira da a gaggauta dawo da ma’aikatan da aka kora ba tare da wani sharadi ba, ta kuma buƙaci kamfanin ya bayar da uzuri a bainar jama’a tare da tabbatar da cewa ba za a sake cin zarafin ma’aikata ba.
Haka kuma ta nemi a gudanar da bincike mai zaman kansa da ya haɗa da ma’aikatar ƙwadago, ƙungiyar ILO da sauran masu ruwa da tsaki kan yadda ake tafiyar da harkokin ƙwadago a kamfanin.
Labari mai alaƙa: Gwamnatin tarayya ta gayyaci PENGASSAN da kamfanin Dangote zuwa zaman sulhu don tabbatar da zaman lafiya
Kungiyar ta yi gargaɗi cewa za ta ɗauki mataki mai tsanani idan kamfanin Dangote bai amsa buƙatunta cikin lokaci ba.
Hakan na iya kaiwa ga gudanar da yajin aiki na ƙasa baki ɗaya daga mambobin ƙungiyarta a faɗin ƙasar nan.
Sai dai a gefe guda, hukumar gudanarwar kamfanin sarrafa mai na Dangote ta ce korar ma’aikatan wani ɓangare ne na sake fasalin ayyuka bayan samun matsalolin da suka shafi tsaro a masana’antar.
A cikin wata takarda da aka fitar ranar 24 ga Satumba, 2025, wacce babban manajan kula da ma’aikata, Femi Adekunle, ya sanya wa hannu, kamfanin ya ce ya zama tilas ya aiwatar da sabon tsarin aiki saboda yawaitar abubuwan da aka ruwaito na ɓata tsaron masana’antar.













































