Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya mika sunayen mutane 32 ga majalisa Dattawa wadanda ya tsayar domin nada su a matsayin jakadu jim kadan bayan turo jerin farko na mutane uku.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban kasa Bayo Onanuga ya sanya hannu.
Sanarwar ta bayyana cewa shugaban kasar ya roki majalisar dattawa ta hanzarta tantance mutane 15 a matsayin jakadu na aiki da kuma mutane 17 a matsayin jakadu marasa aikin gwamnati.
A jerin jakadu marasa aikin gwamnati akwai Barrister Ogbonnaya Kalu daga Abia, tsohon mai ba da shawara ga shugaban kasa Reno Omokri daga Delta, tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta Mahmud Yakubu, tsohuwar uwargidan jihar Ekiti Erelu Angela Adebayo, da tsohon gwamnan jihar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi.
Sauran sun hada da Tasiu Musa Maigari tsohon shugaban majalisar dokoki ta Katsina, Yakubu N. Gambo tsohon kwamishina a Filato, da tsohon mataimakin sakatare na hukumar ilimi ta asali. Haka kuma akwai Farfesa Nora Ladi Daduut daga Filato, Otunba Femi Pedro tsohon mataimakin gwamnan Legas, Femi Fani-Kayode tsohon ministan sufurin jiragen sama daga Osun, da Barrister Nkechi Linda Ufochukwu daga Anambra.
A jerin wadanda za su zama jakadu na aiki akwai Enebechi Monica Okwuchukwu daga Abia, Yakubu Nyaku Danladi daga Taraba, Miamuna Ibrahim Besto daga Adamawa, Musa Musa Abubakar daga Kebbi, Syndoph Paebi Endoni daga Bayelsa, Chima Geoffrey Lioma David daga Ebonyi da Mopelola Adeola-Ibrahim daga Ogun.
Sauran sun hada da Abimbola Samuel Reuben daga Ondo, Yvonne Ehinosen Odumah daga Edo, Hamza Mohammed Salau daga Neja, Ambassador Shehu Barde daga Katsina, Ambassador Ahmed Mohammed Monguno daga Borno, Ambassador Muhammad Saidu Dahiru daga Kaduna, Ambassador Olatunji Ahmed Sulu-Gambari daga Kwara da Ambassador Wahab Adekola Akande daga Osun.
Ana sa ran sabbin jakadu za su wakilci Najeriya a kasashe da ke da muhimman dangantaka da kasar, kamar China, Indiya, Koriya ta kudu, Kanada, Makziko, Daular Larabawa, Qatar, Afirka ta kudu, Kenya, da kuma manyan hukumomin duniya irin su Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO da kungiyar Tarayyar Afirka.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa za a fitar da karin sunaye nan gaba.













































