Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike na gaskiya kuma gamsasshe kan mutuwar mutanen da ake zargi da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba wadanda ke tsare a hannun Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) a Jihar Neja.
Ya bayar da umarnin cewa a kamo tare da gurfanar da duk wani jami’in da aka samu da hannu wajen haddasa mutuwar tasu.
Read also: Gwamnatin Kano ta rusa cibiyar kasuwanci ta jihar, ta kafa kwamitin riko
Shugaban, a cikin wata sanarwa da Babban Taimakonsa na Musamman kan Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa rahotan mutuwar babban lamari da ke bukatar bincike na gaggawa da kuma tabbatar da adalci.
Ya ce rayuwar kowane dan Najeriya tana da kima, kuma bai kamata wani dan kasa ya mutu a tsare ko hannun gwamnati sakamakon sakaci, cin zarafi, wulakanci ko rashin gudanar da aiki yadda ya kamata ba.
“Idan bincike ya tabbatar da cewa wani jami’i, ta hanyar aikata wani abu, cin zarafi ko sakaci, ya taimaka wajen faruwar wadannan mace-mace, dole ne a kama wannan jami’in kuma a gurfanar da shi gaban kotu daidai da doka. Dole ne a tabbatar da gaskiya da adalci,” in ji Shugaban.
Tinubu ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da yaki da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da sauran ayyukan laifi, sai dai ya jaddada cewa dole ne ayyukan tabbatar da doka su bi ka’ida kuma su girmama hakkokin mutanen da ke tsare.
Read also: Shugaban Senegal ya zama sabon shugaban ECOWAS
“Kasancewar ana zargin wadannan mutane da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, hakan ba zai taba tauye hakkinsu na rayuwa, mutunci, da kuma kyakkyawar kulawa ba yayin da suke tsare a hannun gwamnati.
Gwamnati ba za ta amince da mace-mace masu yawa da ke tasowa daga sakacin jami’ai, gaza gudanar da aiki, ko gazawar ma’aikatan gwamnati wajen kare rayukan da aka danka musu amana ba,” in ji shi.
Shugaban ya ba da umarnin cewa binciken ya shafi yanayin da aka yi kamen, yanayin da fursunonin suke ciki lokacin da aka tsare su, yanayin wurin da aka tsare su, yawan mutanen da aka tsare a ginin, kulawar lafiya da aka ba su, da kuma abubuwan da suka kai ga mutuwarsu.
Haka kuma ya yi gargadin cewa dakatar da jami’ai kada a dauke shi a matsayin madadin gano ko akwai laifin kisa ko laifi na karkashin doka.
“Dakatar da jami’ai mataki ne kawai na tsaro na gudanarwa, kuma kada ya zama madadin ingantaccen bincike na gano laifi da hukunci idan har hujjoji sun nuna bukatar gurfanarwa,” in ji Tinubu.
Read also: Iran ta ayyana zaman makoki na kwanaki 40 bayan rasuwar Khamenei
Shugaban ya umarci Ma’aikatar Cikin Gida da shugabancin hukumar NSCDC da su ba da hadin kai dari bisa dari ga hukumomin bincike da abin ya shafa, sannan su tabbatar babu wani jami’i da zai tsoma baki cikin binciken ko kuma ya kawo cikas ga kokarin gano gaskiya.
Wadannan mace-mace sun faru ne bayan an kama mutanen da ake zargi da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba yayin gudanar da ayyukan tabbatar da bin doka a yankin Wushishi da Lukoto na Jihar Neja a ranakun 15 da 16 ga watan Satumba.












































